Sojin Kenya sun kai farmaki a Somaliya

taswirar Kenya da Somalia Hakkin mallakar hoto 1
Image caption taswirar Kenya da Somalia

Sojin Kenya sun ce sun kai wani hari ta sama a kan wani kauyen Somalia a kusa da kan iyaka da Somaliar.

Wani kakakin sojin Manjo Emmanuel Chirchir, ya ce sun gudanar da samame biyu a wani sansanin kungiyar nan ta Islama, Al- Shabaab, a kauyen Hosingow kusan kilomita casa'in daga kan iyaka.

Manjo Chirchir ya ce sun kashe 'yan gwagwarmayar Islaman sha bakwai.

Ya kuma kara da cewa, a wannan sansani kadai akwai mayakan Al-Shabaab fiye da ashirin da shidda, akwai manyan kwamandojin Al-Shabaab da tsohon jami'in mulki na Al-Shabaab a yankin.

Ya dai musanta zargin da Al-Shabaab ta yi cewar an kashe fararen hula sha daya.

A cikin watan Oktoba, Kenya ta aike da dakaru zuwa tsallaken kan iyaka don fatattakar kungiyar ta Al-Shabaab.

Karin bayani