Pira Minitan Pakistan ya soki sojin kasar

Pira Ministan Pakistan Gilani Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Pira Ministan Pakistan Gilani

Praministan Pakistan, Yousouf Raza Gilani, ya yi zargin cewa masu zagon kasa na shirin kifar da gwamnatinsa.

Gilani ya kuma bayyan cewa tilas ne sojojin kasar su kasance karkashin majalisar dokokin kasar.

Wannan shi ne karon farko da Mr Gilani ke fitowa karara yana bincikar rawar da sojojin kasar ke takawa.

Jawabin na sa ya biyo bayan tsegunta wata takardar gwamnatin da ake zargin an nemi taimakon Amurka na ta kare gwamnatin Pakistan daga yiwuwar yi mata juyin mulki.

Wakilin BBC a Pakistan ya ce ba'a gano ko wa ye ya rubuta takardarba, kuma a ranar Juma'a ne kotun kolin kasar za ta fara saurarar wata kara akan batun.

Har ila yau Mr Gilani ya yi tsokaci kan takaddamar da ake kan yadda jagoran kungiyar Al-qaeda, marigayi Osama Bin Laden, ya zauna a Pakistan har tsawon shekaru shida ba tare da gwamnati ta sani ba.

Neman afuwa

Amurka ta bayyana takaicinta da kuma ta'aziyyarta dangane da harin da kungiyar NATO ta kai wanda ya yi sanadiyar kashe sojojin Pakistan ashirin da hudu.

Kasar ta kuma amince an aikata kurakurai da dama.

Bayyana takaicin da Amurkan ta yi, ya biyo bayan binciken da rundunar sojan kasar ta yi ne, wanda ya nuna cewa sojin Amurkan sun kare kansu ne bayan an kai musu hari a kan iyakar Pakistan da Afghanistan.

Sai dai sun amince da cewa ba a samu hadin kai da sojin Pakistan ba wajen yadda al'umra suka gudana a ranar.

Kasar pakistan dai ta mayar da martani cikin fushi, inda ta rufe kan iyakokinta da Afghanistan ga motocin NATO da ke kai kayan tallafi ga sojojinta da ke Afghanistan.

Karin bayani