Muhawara kan janye tallafin mai a Najeriya

Wata mata mai saida kaya a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata mata mai saida kaya a Najeriya

Kungiyar masu kamfanonin jaridu ta Najeriya, ta shirya wata muhawara akan shirin gwamnatin kasar na cire kudaden tallafin da take zubawa a harkar samar da man fetur.

A wajen muhawarar masu goyon bayan janye tallafin da suka kunshi manyan jami'an gwamnati, sun ce tallafin yafi amfanar wasu manyan mutane ne a kasar da kuma kasashen dake makwabtaka da Najeriya.

Amma a daya banagaren, masu adawa da janye tallafin na cewa idan har gwamnati na son dorawa al'umma nauyi, to akwai bukatar gwamnati ita ma ta sadaukar da wasu kudaden da take kashewa don jin dadin jami'anta.

Taken muhawarar shi ne janye tallafin man fetur wa ye zai ci gajiyarsa.

A dandalin muhawarar, ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonjo Iweala ta fara shimfida ne da abinda ta kira bayanai game da tallafin man fetur don masu muhawarar su yanke shawarar goyon baya ko rashin goyon bayan janye tallafin.

Ta bayyana cewa masu cin gajiyar tallafin man sun hada da wasu manyan mutane a kasar da wasu daga cikin 'yan kasuwan dake harkar mai, da kasashen dake makwabtaka da Najeriyar da kuma masu fasa kwauri.

A nasa bangaren mataimakain shugaban kungiyar kwadago na kasar Mr. Isa Aremu, ya ce maganar daina zuba tallafi bata taso ba domin ko a kasashen yamma kamar su Burtaniya babu wani dan siyasa da ya isa ya taba kudaden tallafi na kiwon lafiya na NHS.

Ya kuma kara da cewa, za su iya fahimtar cewa gamnati bata da kudaden da za ta cigaba da zuab tallafin, amma abin yi shi ne neman wasu hanyoyi na samun wadannan kudade.

Ya ce: "Akwai bukatar gwamnati ta sadaukar da wasu abubuwa, a kaddara kowane gwamna daya na da kudaden da aka ware masa na bangaren tsaro da ya kai miliyan dubu uku, shin a cikinsu akwai wanda yace bari in zuba kashi hamsin cikin dari na kudin a wannan asusu."

Sai dai shugaban babban bankin Najeriyar Sanusi Lamido sanusi ya ce sun amince cewa akwai bukatar gwamnati ta rage kudaden da take kashewa, amma idan aka cigaba da sanya kudade a tallafin man fetur da ake amafani da shi a cikin gida, abinda ake yi shi ne bude harkokin mai a kasashen waje, samar da ayyukan yi a can, kuma abinda ya kamata kungiyar kwadago ta hana ke nan. Ta bada goyon baya wajen sanya tallafi a harkokin mai na cikin gida.

Shi ma Ben Bruce wani mai gidan talabijin na Silverbird ya bayyana irin waharlar da talakwa za su shiga idan aka janye tallafin, inda ya kara da cewa rashin ingantaccen tsarin sufuri a kasar zai assasa matsalar.

A halin yanzu dai mutanen Najeriya na biyan naira 65 akan litar mai daya kuma janye tallafin zai sa su rinka biyan abinda zai iya kaiwa naira 140.

Muhawarar dai ta zo ne a lokacin da ake ciaga da cece kuce game da janye tallafin mai a kasar.