'Shugaba Assad ba shi da wani halacci'

Shugaba Bashar al-Assad Hakkin mallakar hoto AFP SANA
Image caption Shugaba Bashar al-Assad

A daya daga cikin sanarwoyi mafi zafi da ta fitar a kan Syria, Amurka ta ce shugaba Bashar al-Assad ya rasa duk wani halacci da kimar da yake da ita.

Fadar gwamnatin Amirkan ta White House ta ce, ta damu matuka game da rahotanni masu tushen da ake samu, wadanda ke cewa ana yiwa fararen hula da kuma sojojin da ke fandarewa kisan mai uwa da wabi.

Ta bukaci a aiwatar da shirin zaman lafiya na kungiyar kasashen Larabawa ba tare da bata lokaci ba.

Ta yi gargadin cewa, idan hakan bai samu ba, to kwa za a sa wa mahukuntan Syriar wani sabon takunkumi.

Kungiyoyin adawa sun ce mutane fiye da 200 ne aka kashe a kwanaki biyun da suka wuce a Syriar.

A gobe ake sa ran kungiyar kasashen Larabawan za ta aike da wata tawagar 'yan kallo zuwa Syriar, domin kula da yadda za a kawo karshen tashin hankalin.

Karin bayani