BBC navigation

Bama-bamai sun tashi a Iraqi

An sabunta: 22 ga Disamba, 2011 - An wallafa a 16:34 GMT

Akalla mutane sittin da uku ne suka mutu sanadiyar tashin bama baman

Jami'ai a Iraqi sun ce kimanin mutane sittin da uku ne suka mutu yayin da fiye da mutane dari biyu suka samu raunuka sakamakon tashin wasu bama-bamai a Bagadaza babban birnin kasar.

Ministan harkokin cikin gida na kasar ya shaidawa BBC cewa an kai hare haren ne a wasu wurare goma sha uku a babban birnin kasar.

Kawo yanzu dai babu wasu da suka dauki alhakin kai hare haren da suka abku 'yan kwanaki kafin rukunin karshe na sojojin Amurka su kammala janyewa daga Iraqi.

Haka kuma wadannan hare haren sun abku ne a dai dai lokacin da rikicin siyasa ya barke a kasar bayan da aka bayar da sammacin kame mataimakin shugaban kasar Tareq al- Hashimi, wanda shine dan siyasa mafi girman mukami a tsakanin 'yan siyasa mabiya sunni dake kasar.

Shugaban daya daga cikin manyan kabilun 'yan Sunni a Iraqi, Ali Hatem Suleiman, ya bi sahun sauran shugabannin Sunni na kasar wajen kwatanta Pira Ministan kasar Nuri al-Maliki da Saddam Hussein, yana mai cewa yana kokarin maida kasar karkashin mulkin kama karya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.