Mutane fiya da 1000 sun bace a Philippines

Image caption Ambaliya ruwar da ta sanadiyar mutuwar mutane da dama

Har yanzu ba a san inda mutane fiye da dubu daya suke ba a Philippines, kusan mako guda bayan wata iska da ruwa ta haddasa ambaliyar da ta yi kacakaca da tsibirin Mindanao.

Wadannan alkaluma dai sun haura kiyasin da aka yi a baya nesa-ba-kusa b.

Sai yanzu ne dai wasu iyalan da ke yankunan karkara ke kai rahoton cewa har yanzu ba su ga danginsu da ke aiki a biranen da abin ya shafa ba.

An dai hakikance cewa ambaliyar ruwan ta yi sandiyyar mutuwar mutane fiye da dubu daya.

Wani jami'in tsaro ya ce ambaliyar ta hallaka wasu iyalai gaba dayansu a wasu garuruwa biyu masu.

Karin bayani