Masu sa ido sun isa Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jana'izar wadanda aka kashe a Syria

Rukunin farko na masu sa ido daga Kungiyar Kasashen Larabawa ya isa Syria a karkashin wani shiri na kawo karshen murkushe masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Tawagar dai za ta sa ido ne a kan yadda kasar ta Syria ke aiwatar da tanade-tanaden shirin na samar da zaman lafiya wanda ya bukaci a janye sojoji daga kan tituna, a saki fursunoni, sannan a hau teburin shawarwari da 'yan adawa.

Sai dai wani dan rajin tabbatar da dimokuradiyya a birnin Homs ya shaidawa BBC cewa tuni gwamnatin ta fara shirin yaudarar masu sa idon.

Ya ce gwamnatin kasar na kai tankokin yaki da motoci masu sulke can bayan gari, suna boyesu a kan tsaunuka, sai masu sa idon sun bar Homs sannan su dawo da su.

Gwamnatin kasar Amurka ta ce Shugaban kasar, Bashar al-Assad a yanzu haka bashi da kima a duniya kuma ya rasa duk wani hallaci.

Amurka dai ta nuna damuwa game da irin rahotannin dake fitowa daga kasar wanda ke nuni da cewa ana ci gaba da kashe fararen hula da kuma sojojin da su ka sauya sheka ba kaukautawa.

Amurka dai ta yi kira da a gaggauta aiwatar da kudirin zaman lafiya da kungiyar kasashen Larabawa ta tsarawa kasar, Sannan kuma ta ce muddin ba a yi hakan ba, a shirye take ta kara kakkabawa kasar sabbin takunkumi.

Kungiyoyin 'yan adawa a kasar dai sun ce an kashe sama da mutane dari biyu a kasar a cikin kwanaki biyu.

Gwamnatin Syria dai ta nace cewa tana yaki ne da 'yan ta'ada dake kokarin kifar da gwamnatin ta.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce sama da mutane dubu biyar ne suka rasa rayukansu tun da aka fara zanga-zangar kin jinin gwamnati a watan Mayu.

Karin bayani