Ana neman Jean Claude Mas ruwa a jallo

mas Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jean Claude Mas na fuskantar zargin na zamba

'Yan sandan kasa da kasa na kokarin damke wanda ya kirkiro da wani kamfani da aka rufe mai suna PIP a Faransa, saboda sayarda abubuwan yin dashen mama, mara inganci ga dubban mata a duniya.

'Yan sanda na kasa da kasa sun ce jami'ai a kasar Costa Rica suna neman Jean Claude Mas, ruwa a jallo saboda wasu laifuka da suka shafi kiwon lafiya.

An sayarda da kayan kamfanin sosai a yankin Latin Amurka da Turai.

Kamfanin Jean Claude Mas mai suna PIP a baya shine na uku mafi girma a duniya dake samarda akalla kayayyakin dashen mama dubu dari a duniya.

A bara aka rufe kamfanin bayan ya sayarwa dubban mata kayayyakinsa a kasashe kusan sittin da biyar.