Raul Castro na Cuba zai saki fursunoni 3000

castrp Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Cuba Raul Castro

Kasar Cuba ta ce zata saki fursinoni akalla dubu uku cikin 'yan kwanaki masu zuwa hadda 'yan kasashen waje.

Shugaban kasar Raul Castro ya alakanta wannan karamcin ne da ziyarar Papa Roma Benedict zuwa kasar a farkon wannan shekarar da kuma alfarmar da iyalan wanda ake tsare dasu suka nema.

Ya kara da cewar wasu daga cikin wadanda za a sakin mata ne da kuma tsaffi.

Mista Castro a jawabinsa da majalisar dokokin kasar ya ce, daga cikin fursunonin akwai 'yan kasashen waje su tamanin da biyar wadanda suka fito daga kasashe ashirin da biyar.

Sai dai shugaban mai bayyana takkamammen wadanda suka samu afuwar ba.

Karin bayani