An kashe Yansanda ukku a wani artabu a Najeriya

Yansanda a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yansanda a Najeriya

Yansanda a Najeriya sun yi ta kafsa wani artabu da bindigogi a arewa maso gabacin kasar tare da yan kungiyar masu tsatstsauran kishin Islama.

Kwamishinan Yansanda na Jihar Yobe, Lawan Tanko ya ce, fadan ya faru ne da daren jiya alhamis zuwa safiyar yau Juma'a a Damaturu babban birnin jihar.

Yansanda akalla 3 ne aka kashe a fadan.

Hare haren bama bamai da kuma bindigogi sun faru a jerin birane a cikin arewacin Najeriya yayinda Gwamnati ke kokarin murkushe Kungiyar Islaman nan ta Boko Haram.

Karin bayani