Tashin bama-bamai a Damaturu da Maiduguri

Bam ya tashi a Damaturu da Maiduguri
Image caption Bam ya tashi a Damaturu da Maiduguri

An samu tashin bama-bamai da harbe-harbe a wasu birane na arewacin Najeriya, wadanda suka haddasa mutuwar akalla mutum guda.

An ji tashin bam na farko ne a Damaturu, inda wani ma'aikacin asibiti ya ce soja daya ya rasa ransa, yayinda wasu 'yan sanda kuma suka jikkata.

Daga bisani kuma an ba da rahoton cewa mazauna birnin Maiduguri na tserewa yayin da wasu bama-bamai shida suka tashi.

A Potiskum ma an ji harbe-harbe, an kuma ba da rahoton tashin gobara a wani gini da ke da caji-ofis.

Har yanzu dai ba a tabbatar da wanda ya kai harin ba, amma kuma a baya biranen sun fuskanci tashe-tashen hankulan da ake alakantawa da kungiyar Boko Haram.

Karin bayani