An kashe mutane fiye da arba'in a wani harin kunar bakin wake a Syria

Harin bam a Syria Hakkin mallakar hoto s
Image caption Harin bam a Syria

Jami'an gwamnatin Syria sun ce wasu 'yan kunar bakin wake a cikin motoci biyu sun kashe mutane fiye da arba'in a wasu hare hare da aka kai wa hukumomin tsaro a Damascus babban birnin kasar.

An nuna hotunan ma'aikatan ceto na ta kwashe buraguzai daga hedikwatar ma'aikatar tsaro; inda aka kaiwa wani gini dake kusa da wajen harin shima.

Gidan talabijin din kasar ta Syria ya ce binciken farko ya gano hannun kungiyar al -qaeda a harin.

Sai dai kuma wakilin BBC a yankin ya ce masu fafutukar kin jinin gwamnati na zargi da hannun gwamnati a ciki.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Syria, Jihad Macdashee ya shaidawa BBC cewa kwanaki biyun da suka wuce sun samu gargadi daga Labanon, amma zai yi wuya ka kare kai irin wadannan hare haran.

Karin bayani