An kashe sama da jami'an tsaro bakwai a Damaturu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yansandan Najeriya

Rahotanni daga arewacin Najeriya na cewa sama da mutane hamsin ne aka kashe a fadan da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da masu tsatstsauran ra'ayin Islama. Kwamishinan 'yan sandan jahar Yobe ya ce an kashe 'yan sanda bakwai da sojoji biyu a bata kashin da akai ranar juma'a a garin Damaturu, babban birnin jahar Yobe---- yayin da su kuma sojojin suka kashe sama da 'yan Boko Haram hamsin. Wani da ya ganewa idanunsa abin da ya faru ya shaidawa BBC cewa harbe harban da akai ta yi da kuma tashin bama-bamai ya sa mutane da dama ficewa daga Damaturu

Karin bayani