BBC navigation

An kashe sama da jami'an tsaro bakwai a Damaturu

An sabunta: 24 ga Disamba, 2011 - An wallafa a 14:34 GMT
'Yansandan Najeriya

'Yansandan Najeriya

Rahotanni daga arewacin Najeriya na cewa sama da mutane hamsin ne aka kashe a fadan da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da masu tsatstsauran ra'ayin Islama.

Kwamishinan 'yan sandan jahar Yobe ya ce an kashe 'yan sanda bakwai da sojoji biyu a bata kashin da akai ranar juma'a a garin Damaturu, babban birnin jahar Yobe---- yayin da su kuma sojojin suka kashe sama da 'yan Boko Haram hamsin.

Wani da ya ganewa idanunsa abin da ya faru ya shaidawa BBC cewa harbe harban da akai ta yi da kuma tashin bama-bamai ya sa mutane da dama ficewa daga Damaturu

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.