Yarima Philip na samun sauki

Yarima Philip, maigidan sarauniyar Ingila Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yarima Philip, maigidan sarauniyar Ingila

Iyalan masarautar Birtaniya, na zuwa duba maigidan sarauniyar Ingila, Yarima Philip, wanda ke kwance a asibiti bayan anyi masa tiyata a zuciyarsa. Sarauniya Elizabeth da 'yayanta maza da mace daya dukkansu sun je asibitin dake kusa da garin Cambirdge, inda yarima Philip ke jinyar aikin da akai masa na toshewar wani bangare na zuciyarsa:

Wakiliyar BBC ta ce wannan itace ziyara ta farko da akai kaiwa yarima Philip tun bayan da aka akai shi asibitin a jiya.

Yanzu haka dai ance yana samun sauki. Sai dai kuma ba'a tabbatar ko zai iya zuwa Sand-ringham domin yin bikin kirsimeti tare da sauran iyalan masarautarba kamar yadda aka saba.

Karin bayani