Mutane da dama sun rasa rayukansu a hare-hare a Madalla, Jos da Yobe

'Yansandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yansandan Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane da dama ne suka rasa rayukansu a wasu hare-haren bama-bamai da aka kai Lahadi a Madalla, Jos da Yobe.

An kuma garzaya da wasu mutanen da dama da suka ji raunuka zuwa asibitoci dabam-daban, yayainda ake ci gaba da tattara bayanan yawan wadanda suka rasa rayukansu.

Harin ya auku ne kusa da Cocin St. Theresa da ke Madalla inda masu ibada suka taru domin bukukuwan Kirsimeti.

An dai tsaurara matakan tsaro a yankin.

Wasu bayanan na cewa an samu tashin wani bom din a garin Jos babban birnin jihar pilato.

Rahotanni daga jihar Yobe ma na cewa mutane da dama ne suka rasa rayukansu a wani harin da aka kai a can.

Harin na zuwa ne kwanaki bayan fiye da mutane hamsin sun rasa rayukansu a wani fadan da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram. Kwamishinan 'yan sandan jahar Yobe ya ce an kashe 'yan sanda bakwai da sojoji biyu a bata kashin da aka yi ranar Juma'a a garin Damaturu, babban birnin jahar Yobe yayin da su kuma sojojin suka ce sun kashe sama da 'yan Boko Haram hamsin. Wani da ya ganewa idanunsa abin da ya faru ya shaidawa BBC cewa harbe harben da aka yi ta yi da kuma tashin bama-bamai ya sa mutane da dama ficewa daga Damaturu.

Vatican ta yi Allah wadai

Fadar Vatican ta yi tir da tashin bama-baman da aka samu a Najeriya da cewa abu ne mara ma'ana kuma ta'addanci ne da zai rura wutar gaba.

Duk da cewa a jawabin da ya saba yi kowace ranar Kirsimeti a dandalin St Peter dake fadar Vatican, Paparoma Benedict bai ambaci hare-haren na Najeriya ba, amma wata sanarwa da ta fito daga fadar ta Vatican, ta bayyana hare-haren a matsayin zalunci kuma abu ne da bai mutunta ran dan adam ba.

Mai magana da yawun fadar ta Vatican Rev. Federico Lombardi, ya ce cocin katolika na yi wa 'yan Najeriya addu'a domin su samu damar kawo karshen abin da cocin ya kira aikace-aikacen ta'addanci.

Sanarwar ta fadar Vatican, ta ce an riga an shirya jawabin Paparoman ne tun tuni shi ya sa bai ambaci harin ba.

Karin bayani