An yankewa Chen Xi daurin hukuncin shekaru 10

Chen Xi Hakkin mallakar hoto bbcchinese.com
Image caption Chen Xi ya ce ba zai daukaka kara ba

Wata kotu a China ta yankewa tsohon mai fafatuka Chen Xi hukuncin daurin shekaru goma a gidan kaso saboda raina karfin gwamnati.

Matarsa da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce kotun dake kudancin birnin Guiyang ta yankewa mista Chen hukuncinne saboda kasidu 36 daya wallafa a shafin intanet.

Kasidun sun bada shawarwari ne akan yadda za ayi garan bawul na siyasa da kuma inganta kare hakkin bil adama.

A cewar matar Mista Chen, ya ce shi baida wani laifi amma kuma ba zai daukaka kara ba akan hukuncin daurin.

Mista Chen na cikin mutanen da suka yi wata zanga zanga a kasar a shekarar 1989.

Karin bayani