Duniya ta yi Allah wadai da harin Bom a Najeriya

bom Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane akalla arba'in sun mutu a harin ranar Kirismeti

Ana cigaba da Alla wadai a duk fadin duniya sakamakon hare haren bomb da aka kai ranar Kirismeti a Najeriya inda mutane akalla 40 suka mutu.

Fadar White ta Amurka ta bayyana harin a matsayin tashin hankali mara tunani, kuma ta ce zata taimakawa Najeriya a hukunta wadanda suka aikata.

Birtaniya da Jamus sun bayana harin a matsayin aikin matsorata a yayinda fadar Vatican ta bayyana a matsayin hari na 'yan ta'adda muraran.

Shi kuwa Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan cewa yayi harin wani mataki ne na hana mutane 'yancinsu na walwala.

Rabaran Achi Isaac shine shugaban mabiyar Catolika na Minna "An kashe mutane na da dama sakamakon harin Bam din. A lokacin dana isa wajen naga hayaki ya turnike ga motoci nan wasu sun kone a cikinsu, akwai motar da iyalan gida daya su biyar sun kone kurmus a ciki".

Kungiyar Boko Haram dai ta dauki alhakin kai hare haren.

Karin bayani