Tawagar kasashen larabawa ta isa Syria

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Babbar tawagar yan kallo ta kungiyar kasashen Larabawa ta isa Syria don sa ido a kan wata yarjejeniyar kawo karshen ci gaba da tashin hankaln da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tun somin zanga zangar kin jinin gwamnati a farkon shekarar nan.

Akalla mutane 18 ne aka bayar da rahoton an kashe a ruwan harsasan da ake yiwa Birnin Homs a baya bayan nan.

Shirin da aka amince da shi tare da Gwamnatin Syria ya bukaci dukanin rundunonin soji da su janye daga yankunan rikici.

Shugabannin 'Yan adawar Syria sun bukaci masu sa idon da su je Homs ba tare da wani bata lokaci ba, wani kiran da Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta jaddada.

Syria dai ta ce masu sa idon za su kasance da yancin zuwa duk inda suke so.

Karin bayani