Ganawa tsakanin Jonathan da Sultan

Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar

Kwanaki biyu bayan hare-haren da suka hallaka mutane da dama a Najeriya ranar bukukuwan Krimeti, Sarkin Musulmi, Mai martaba Alhaji Sa'ad Abubakar ya gana da shugaban kasar, Goodluck Jonathan a fadarsa ta Aso Rock dake Abuja.

A lokacin da yake bayani ga manema labarai bayan ganawar, Sarkin Musulmi Mai Martaba Alhaji Saad Abubakar ya fito ya yi Allah Wadai da hare-haren da ake kaiwa a Arewacin Najeriya, yana mai cewa Musulunci ba ya goyon bayan tashin hankali.

Mai Martaba Alhaji Saad Abubakar ya ce a tattaunawar da suka yi da shugaba Jonathan, sun amince cewa daya daga cikin hanyoyin tinkarar wannan al'ammari shi ne a waiwaiyi shawarwarin da kwamitocin da gwamnati ta kafa a kan Boko Haram da kuma rikicin jihar Pilato, suka bayar domin a aiwatad da su cikin gaggawa.

Kimanin mutane ashirin da bakwai ne aka kashe sakamakon harin bam din da aka kai wata majami'a dake garin Madalla.

Karin bayani