Tawagar Larabawa ta isa Syria don magance rikici

syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tawagar larabawa a Syria

Babbar tawagar masu sa ido ta kungiyar kasashen Larabawa ta isa kasar Syria don lura da tsarin kawo karshen tashin hankalin da yayi sanadiyar rasuwar dubban mutane, tun lokacin da aka soma zanga zangar kin jinin gwamnati a farkon wannan shekarar.

Akalla mutane goma sha takwas ne suka mutu sakamakon luguden wuta ta sama na baya-bayannan a birnin Homs.

Kungiyar kasashen larabawa ta amince tsakaninta da gwamnatin Syria akan cewar duka jami'an tsaro za a janye su daga yankunan da ake tashin hankali.

'Yan adawa dai sun bukaci masu sa idon su garzaya birnin Homs ba tare da bata lokaci ba.

Wani mazaunin Baba Amr dake Homs ya shaidawa BBC cewar "sun kewa ye mu ta kowace kusurwa, wasunmu na kokarin zuwa gidajen da aka lalata don mu duba wadanda suka tsira da rayukansu saboda an lalata gidaje da dama."

Karin bayani