An yi zanga-zanga a birnin Homs na Syria

Masu zanga-zanga a birnin Homs Hakkin mallakar hoto amvid capture
Image caption Masu zanga-zanga a birnin Homs

Dubun dubatar jamaa sun yi zanga-zangar nuna kyamar gwamnati a birnin Homs na Syria yayinda wata tawagar 'yan kallo na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ke ziyara a birnin don sa a ido a kan yadda ake aiwatad da wata 'yarjejeniyar zaman lafiya.

Mazauna wata unguwa da suka fusata sunh nuna wa tawagar 'yan kallo wuraren da aka zubar da jini, tare da yin kira garesu da su fadawa gwamnatin Syriar gaskiya.

An dai ji karar harbin bindigogui a lokacin ziyarar.

Masu fafitika sun zargi gwanatin Syriar da boye tankokin yaki a wajen birnin na Homs, don kada 'yan kallon na kungiyar kasashen Larabawa su gansu.

Karin bayani