Shugabar Argentina na fama da cutar daji

Shugaba Cristina Fernandez ta Argentina Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cristina Fernandez ta Argentina na fama da cutar daji

An bada sanarwar cewar Shugaba Cristina Fernandez ta Argentina na fama da cutar daji, kuma za a yi mata tiyata a mako mai zuwa.

Gwamnatin Kasar Argentinan ta ce Shugabar ta kamu da cutar dajin a makogaranta, amma bata bazu zuwa sauran sassan jikinta ba.

A kwanan nan ne dai Ms Fernandez ta soma wa'adinta na biyu na mulki a matsayin Shugabar Kasa, bayan nasarar data samu a zaben da aka gudanar.

Shugaba Cristina ita ce Shugabar wata Kasa a Latin Amurka ta baya bayan nan da take fama da cutar daji.

Shugaban Kasar Venezuela Hugo Chavez da shugaban Paraguy Fernando Lugo dama tsohon Shugaban Kasar Brazil Inacio Lula da Silva, duka sunyi fama da cutar daji kuma saida akai masu tiyata

Karin bayani