Ana gudanar da jana'izar Kim Jong il

Jana'izar Kim Jong- il Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana gudanar da gagarumar jana'iza ga Marigayi Kim Jong il

Ana can ana gudanar da wata gagarumar jana'iza a Koriya ta Arewa ga marigayi Shugaba Kim Jong il, wanda ya jima akan karagar mulkin Kasar.

Hotunan talabijin daga titunan birnin Pyongyang lullube da dusar kankara, sun nuna dogon layin masu jana'izar, ga kuma wata bakar mota dake dauke da mutum- mutumin Shugaban kasar Marigayi na yi masu jagora.

Dakarun Kasar dai sun dukar da kawunansu a lokacin da motar ke wuce dubun- dubatar masu alhini, wasu daga cikinsu nata rusa kuka .

Fitattun mutanen da suka halarci jana'izar dai sun hada da dan Mr. Kim wanda kuma zai gaje shi wato Kim Jong Un.

Masu aiko da rahotanni sun ce mahukuntan Koriya ta Arewan zasu yi amfani da wannan lokaci wajen girmama gawar marigayin

Karin bayani