Syria ta sako fursunoni sama da dari bakwai

hoton Pursunoni a Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption hoton Pursunoni a Syria

Gidan Talabijin na Syria ya ce hukumomin kasar sun yanke shawarar sako fursunoni sama da dari bakwai da hamsin dake da hannu a zanga zangar nuna kyamar gwamnati.

Sai wadanda aka sako ba su hada da wadanda rahoton ya kira, wadanda suka zubar da jinin 'yan kasar ta Syria ba.

An dauki matakin ne a rana ta biyu ta ziyarar da masu sa ido na kungiyar kasashen Larabawa ke yi a kasar.

Tun da farko jagoran tawagar ya bayyana halin da ake ciki a birnin Homs da cewa mai karfafa gwiwa ne.

Janar Mustafa al-Dabi ya ce a lokacinda masu sa idon suka ziyarci birnin jiya Talata, al'amurra sun lafa, babu tashin hankali.

Karin bayani