Rikici na ci gaba a kasar Syria

Masu sa ido na kasashen Larabawa Hakkin mallakar hoto Getty Youtube
Image caption Masu sa ido na kasashen Larabawa

An ci gaba da samun tashin hankali a Syria duk kuwa da kasancewar tawagar sa ido ta kungiyar kasashen Larabawa, wadda aka tura da nufin taimakawa a kawo karshen rikicin.

Masu fafutuka sun ce an kashe mutane sama da goma a garuruwan Homs da Dera'a da kuma Idlib, wadanda cibiyoyi ne na nuna adawa da gwamnati.

Wakilin BBC ya ce duk da shakkun da wasu masu fafutuka ke nunawa kan tawagar kasashen Larabawar, bisa dukan alamu masu sa idon sun ratsa ta wasu unguwanni da rikicin ya fi muni a Homs, ba tare da rakiyar jami'an tsaron Syriar ba.

A yau hukumomin Syriar sun ce su saki fursunoni sama da dari bakwai da hamsin, wadanda aka kama bisa alaka da zanga zangar nuna kyamar gwamnati.

Sai dai masu fafutuka na korafin cewa akwai sauran fursunoni sama da dubu arba'in da ake ci gaba da tsarewa.

Karin bayani