Shugaba Jonathan ya gana da jami'an tsaro

harin bama-bamai a Nijeriya
Image caption harin bama-bamai a Nijeriya

Rahotanni daga Nijeriya na cewa shugaba Goodluck Jonathan ya gana da manyan shugabannin hukumomin tsaron kasar, inda ya tattauna da su kan barazanar da ake kara samu ta harkar tsaro, sakamakon hare haren da kungiyar Boko Haram ta amsa kaiwa a kwanakin nan, a kusa da Abuja, da a birnin Damaturu, jihar Yobe, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma raunata wasu.

Daga cikin wadanda suka halarci taron na yau a fadar gwamnatin dake Abuja sun hada da Babban sufeton 'yan sandan Nijeriya, da shugaban hukumar tsaron farin kaya, SSS da babban mai bada shawara ta fuskar tsaro na kasa, da kuma babban hafsan rundunonin tsaron kasar.

Hare haren dai sun janyo kungiyar Kiristoci ta kasa, CAN yin barazanar daukar matakan kare kanta da kuma na daukar fansa, idan lamarin ya ci gaba.

Akwai rahotanni dake nuna cewa shugaba Jonathan zai gudanar da garambawul a majalisar tsaron kasar, sai dai har zuwa karshen ganawar, babu abin da ya bayyana.

Karin bayani