An kama fitaccen dan adawa a Senegal Barthlemy Dias

Shugaba Wade na Senegal Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana tsare da dan- adawar gwamnatin Senegal Barthlemy Dias

Ana tsare wani fitaccen dan adawar nan a Senegal wato Barthlemy Dias watanni biyu kafin gudanar da zaben shugaban kasa.

An tsare Mr Dias wanda shine magajin garin Dakar bayan da aka zarge shi da hadin baki a wani harbi da aka yi a makon daya gabata.

An dai yi harbin ne, bayan da wasu gungun mutane da akai imanin cewar magoya bayan Shugaba Abdulaye Wade ne su kai arangama da magoya bayan Mr. Dias a birnin Dakar.

An dai kashe daya daga cikin masu goyan bayan Shugaban kasar a lokacin artabun.

Magoya bayan Mr Dias dai sunce yana kare kansa ne daga harin da magoya bayan Shugaba Wade suke kai masa.

Ana zaton dai Mr Wade zai tsaya takarar shugaban kasa a wani wa'adi na uku, a watan Fabrairu.

Sai dai 'yan adawa sun ce ba zasu amince ya sake tsayawa takarar ba

Karin bayani