An kashe mutane akalla 40 a Syria

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto na
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Kungiyoyin masu fafutuka a Syria sun ce dakarun gwamnati sun kashe mutane kimanin arba'in ranar Alhamis din nan.

Masu fafutukar sun ce dakarun tsaro sun yi harbi cikin taron jama'a, wadanda suka yi cincirindo a unguwannin da ake kyautata zaton tawagar sa ido ta kungiyar kasashen Larabawa zata kai ziyara, ciki har da wasu unguwanni dake wajen Damascus, babban birnin kasar.

A yau an shirya cewa masu sa ido, wadanda suka fara ziyarar tasu ranar Talata, zasu kai ziyara wasu daga cikin garuruwa da aka fi samun barkewar rikici, da suka hada da Deraa, da Hama da Idlib.

Akwa kuma wadanda suka kai ziyara birnin Homs.

Wani wakilin BBC na cewa kasancewar tawagar masu sa idon ta kara rura wutar rikicin ce, maimakon yayyafa ma ta ruwa.

Karin bayani