Jam'iyyar adawa a Jamaica ta lashe zabe

Ms. Simpson Miler Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jam'iyyar adawa a Jamaica ta lashe kujerun majalisar dokoki

Jam'iyyar adawar Kasar Jamaica ta Peoples National Party karkashin jagorancin Ms Simpson Miller ta lashe babban zaben da aka gudanar.

Yayinda aka bayyana kusan dukkanin sakamakon kuri'un da aka kada, jam'iyyar ta sami kashi biyu bisa ukun kujerun da ake bukata a majalisar dokokin kasar.

Wannan shine zai kasance wa'adin Ms Simpson Miller na biyu a matsayin Fira Ministar Kasar.

Batun tattalin arzikin kasar Japan din kuma shine ya kankame yakin neman zaben ta.

Wakilin BBC ya ce yayinda jam'iyyar dake mulki a Jamaican ke cewa ta daidata tattalin arzikin kasar, 'yan adawa cewa suke bashin da ake bin Kasar ya yi yawa, kuma sun zargi gwamnatin Kasar da rashin gudanar da al'amura yadda ya kamata

Karin bayani