An kai hari wata kasuwa a Maiduguri

An kai hari a wata kasuwa a Mauduguri
Image caption An kai hari a wata kasuwa a Mauduguri

Wani bam ya tashi a wata kasuwa a Maiduguri dake arewacin Najeriya ya kashe mutane hudu tare kuma da jikata wasu.

Wani mai magana da yawun sojoji ya kwatanta tashin bam din a matsayin mai karfin gaske, an kuma dora alhakinsa kan kungiyar masu tsatstsauran ra'ayin Islama ta Boko Haram.

Sai dai kuma daga bisani rundunar hadin gwuiwa ta JTF a Maidugurin ta musanta cewa wani bam ne ya tashi, illa dai wasu ne suke kai hari kasuwar.

Kungiyar ta ce ita ke da alhakin hare-haran ranar kirsimeti, ciki har da wanda aka kai wani coci a kusa da Abuja babban birnin tarayyar Nageriyar, inda akalla mutane arba'in da biyu suka rasa rayukansu.

Karin bayani