An kashe fararen hula fiye da talatin a Syria

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

Dakarun tsaron Syria sun bude wuta a kokarin hana dubban masu zanga zanga a duk fadin kasar nuna adawarsu ga gwamnati a gaban masu sa ido na kungiyar kasashen larabawa.

Masu fafutika sun ce an kashe akalla mutane talatin da biyu a garuruwan da abin ya fi kamari kamar Hama, da Deraa da kuma Homs, wadanda masu sa don suka ziyarta.

Wadanda suka ganewa idanunsu abin da ya faru sun ce sojojin sun yi arangama da dubban masu zanga zangar dake barin masallaci a birnin Damascus.

'Yan adawan sun ce dimbin jamaa sun amsa kiran da suka yi masu na su fito a yi gangami a duk fadin kasar, don nunawa masu sa ido na kungiyar kasashen larabawa irin fushin da suke yi da gwamnatin kasar.

Rahotanni dai na nuna cewa irin damuwar da jama'ar Syriar ke nunawa dangane da tasirin ziyarar ta jami'an kasashen Larabawa, za ta karfafa wa kasashe da dama gwiwa, musamman Amurka, wajen yin tinanin irin matakan da ya kamata su kara dauka, wajen tilastawa shugaba Bashar al Assad, sauka daga kan karagar mulki.

Karin bayani