An kashe mutane arba'in a jihar Ebonyin Najeriya

Wasu sojojin Najeria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu sojojin Najeria

Rahotanni daga jihar Ebonyi dake kudu maso Gabashin Najeriya, sun ce an kashe kimanin mutane 40 a wani fada da aka yi tsakanin 'yan kabilar Eza da na Ezillo.

Haka kuma an ce an yi kone-konen kadarori masu yawan gaske. A yau da safe ne dai rikicin ya barke a garin Ezillo, kuma da ma an jima ana fama da wannan rikici, wanda ke da nasaba da batun bako da dan kasa da kuma na mallakar filaye.

Rundinar 'yan sandan jihar ta Ebonyi tatabbatar da aukuwar rikicin, amma ta ce ya zuwa yanzu ba ta da cikakken bayani kan irin asarar rayika da ta dukiyoyin da aka yi.

Karin bayani