Iran tayi gwajin makamai masu linzami

Mmakamai masu linzami Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Iran ta yi gwajin makamai masu linzami masu cin dogon zango

Rahotanni daga Iran na cewar Kasar tayi gwajin wasu makamai masu linzami da ta harba masu cin dogon zango a yankin Gulf.

Dama Iran tayi ta gudanar da atisayen soji a yankin na Gulf a daukacin makon daya gabata.

Wakilin BBC yace dama Iran tayi barazanar rufe mashigar Hormuz, tana mai cewar babu man da zai wuce idan har gwamnatocin Kasashen yammacin duniya suka aiwatar da shirinsu na sanyawa Kasar karin takunkumi, saboda shirinta na Nukiliya.

Nan take Amurka ta maida martani inda tace wani al'amari ne da zata lamince da shi ba

Karin bayani