An kafa 'dokar ta baci' a wasu sassan Najeriya

Yan sanda a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana dora alhakin tashin hankalin kan kungiyar Boko Haram

Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a wasu sassan kasar sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi a kasar - wadanda ake alakantawa da kungiyar Boko Haram.

Shugaban ya kuma bayar da umarnin a rufe iyakokin kasar da yankunan da abin ya shafa.

"Na yi amfani da ikon da doka ta bani...na kafa dokar ta baci a wadannan kananan hukumomin," kamar yadda ya bayyana a jawabin da yayi ta gidan talabijin na kasar.

Dokar ta bacin za ta shafi wasu kananan hukumomi ne a jihohin Borno da Yobe da Plateau da kuma Naija.

Jihohi da kananan hukumomin da abin ya shafa:

(i) Jihar Borno

a) Karamar hukumar birnin Maidugiri

b) Gamboru Ngala

c) Banki Bama

d) Biu

e) Jere

(ii) Jihar Yobe

a) Damaturu

b) Gaidam

c) Potiskum

d) Buniyadi-Gujba

e) Gasua-Bade

(iii) Jihar Plateau

a) Karamar hukumar Jos ta Arewa

b) Karamar hukumar Jos ta Kudu

c) Barkin-Ladi

d) Riyom

(iv) Jihar Naija

a) Karamar Hukumar Suleja

"Rufe iyakokin na wucin gadi ne kawai domin shawo kan matsalar tsaro, inda za a sake bude su da zarar an samu zaman lafiya," a cewar Jonathan.

Karin bayani