Dauki ba dadi tsakanin masu zanga- zanga da jami'an tsaro a Syria

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

An yi sabon dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar nuna kyamar gwamnatin Syria inda masu fafutika na 'yan adawa suka ce an kashe wasu karin mutane da dama, amma baa tabbatar da adadinsu ba.

Wannan sabon tashin hankali dai ya zo ne a rana ta biyar da tawagar 'yan kallo na kungiyar kasashen Larabawa ke ziyara a kasar ta Syria.

An nuna foton bidiyo na daya daga cikin jami'an a birnin Dera'a, yana amsa cewa ya ga sojojin gwamnati da ke buya kan rufin gine-gine suka harbin mutane.

Sai dai wakilin BBC ya ce daga bisani, shugaban tawagar, Janar Mustafa al Dabi, ya shaidawa BBC cewa abokin aikin nasa ya yi kuskure ne.

Amma wakilin namu ya kara da cewa hakan zai sa masu zanga-zanga su karfafa zargin da suke yi cewa Janar din yana nuna goyon baya ga gwamnatin Syriar.

Karin bayani