Ma'aikatan Kungiyar bayar da agajin Likitoci ta MSF sun bata a Sudan ta Kudu

Tambarin kungiyar bayar da agajin likitoci ta MSF Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambarin kungiyar bayar da agajin likitoci ta MSF

Kungiyar bayar da agajin likitoci ta MSF, ta shedawa BBC cewar ta damu matuka game da ma'aikatanta fiye da 130 a Sudan ta Kudu da suka tsere zuwa daji don gujewa wani hari da dubban mayaka dauke da makamai suka kai.

Garin Pibor ya fada hannun yan kabilar Luo Nuer a jiya asabar, dukkuwa da kasancewar dakarun Majalisar dinkin duniya da kuma na Gwamnati a garin.

Harin na ramuwar gayya ne a kan wani hari da aka kaiwa mayakan Murle, kuma dubban yan kabilar ta Murle sun tsere daga yankin.

Shedu sun ce an kona gine gine da suka hada da gidaje da kuma wani Coci.

Karin bayani