'Yan sanda sun kama masu zanga-zanga a Najeriya

Zanga-zangar adawa da janye tallafin mai a Najeriya Hakkin mallakar hoto facebook
Image caption Batun janye tallafin ya gamu da fushin 'yan kasar da dama

'Yan sanda a Najeriya sun kama wasu daga cikin mutanen da suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da matakin gwamnati na janye tallafin man fetur a Abuja.

Mutane da dama ne daga cikin masu zanga-zangar da suka taru a dandalin Eagles Square, 'yan sanda suka kama ciki har da wani dan jarida - wanda daga bisani suka sako shi.

Da farko jama'ar sun yi burus da yunkurin jami'an tsaron - wadanda suka hada da sojoji, na hana su gudanar da zanga-zangar.

Daga cikin wadanda suka hadu domin zanga-zangar nuna adawa da matakin gwamnatin kasar na janye tallafin man fetur, harda tsohon ministan birnin tarayyar Malam Nasir el Rufa'i da tsohon dan majalisar tarayya Honourable Dino Melaye.

Jama'a sun taru inda suke sanya hannu kan rijistar da ke nuna cewa sun amince su shiga zanga-zanga.

Akwai rahotanin da ke cewa ana gudanar da zanga-zanga a wasu biranen kasar, da suka hada Kano, inda masu fafutuka suka yi alkawarin tsayar da al'amura cik a kasar sakamakon janye tallafin man.

Sun ce janye tallafin zai kara jefa rayuwar jama'a - wadanda yawancinsu talkawa ne cikin mawuyacin hali.

Kungiyoyin kwadago da na farar hula sun sha alwashin gudanar da kasaitacciyar zanga-zanga a ranar Talata.

A jihar Kano ma...

Sai dai kuma Shugabannin kungiyar daliban 'yan asalin jihar Kano sun gudanar da wata kwarya-kwaryar zanga-zanga kan nuna adawarsu da cire tallafin man fetur din.

Daliban wadanda suka ce zanga-zangar ta somin tabi ce, sun ce sun bada sa'o'i 24 ga gwamnatin kasar ta janye matakin ko kuma su gudar da wata gagarumar zanga-zanga ta dukkan dalibai a fadin jihar a ranar Talata.

A yanzu dai ana sayar da man kan naira 145 ko makamancin haka sakamakon yadda kasuwa ta kasance.

Ana ta bangaren Gwamnatin Najeriya ta yi kiyasin cewa za ta samu karin kudaden da suka kai dala biliyan 8 daga janye tallafin, kuma ta ce za ta yi amfani da su ne wurin ayyukan ci gaban kasa.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen samar da danyan man fetur, amma tana shigo da man da take amfani da shi ne daga waje, sakamakon abinda wasu suke dangantawa da rashin ingantattun matatun mai da kuma tashe-tashen hankula.

Karin bayani