Iran ta kara gwada wasu makamai masu linzami

Wani makami mai linzami da Iran ta gwada Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani makami mai linzami da Iran ta gwada

Iran ta ce ta gwada karin wasu makamai masu linzami 2 a wani abunda ake gani tamkar wani gwajin karfin soji ne a ranar karshe ta atisayen sojin ruwa a mashigin ruwa na Hormuz.

Wani Kwamandan sojin ruwan Iran, Mohmoud Mousavi ya ce dukan gwaje gwajen sun samu nasara.

Wani makami mai linzami na harar jiragen ruwa kirar Iran din ya daki wani abunda aka hara, tare kuma da lalata shi.

Faransa ta bayyana gwaje gwajen a matsayin wani abun juyayi.

Karin bayani