Damar sauyi ta samu ga kasashen Korea guda biyu

Shugaban kasar Korea ta Kudu Lee Myung-bak Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban kasar Korea ta Kudu Lee Myung-bak

Korea ta Kudu ta ce sauyin shugabancin kasar Korea ta Arewa mai bin tsarin kwaminisanci ya samar da wata dama ta inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Kasashen biyu dai sun shafe kimanin shekaru sittin su na zaman doya da manja.

Shugaban kasar Korea ta Kudun Lee Myung-bak, ya ce babban burinsa shine samar da zaman lafiya a yankin Korea.

Shugaba Lee ya ce, an samu sauyi, to amma muddin Korea ta Arewa ta aikata wani abu na tsokana, Korea ta Kudu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin maida martani.

Karin bayani

Labaran BBC