Ana kara samun rashin jin dadin jama'a kan tallafin man fetur a Najeriya

An cire tallafin man fetur a Najeriya
Image caption An dade ana cece-kuce kan janye tallafin man fetur a Najeriya

Jami'an tsaro da suka hada da sojoji da yan sanda sun yi kokarin tarwatsa wani yunkuri na gudanar da wata zanga-zanga a dandalin Eagles Square da ke birnin tarayya Abuja.

Daga cikin wadanda suka hadu domin zanga-zangar nuna adawa da matakin gwamnatin kasar na janye tallafin man fetur, har da tsohon Ministan birnin tarayya, Malam Nasir El Rufa'i, da kuma tsohon dan majalisar tarayya, Dino Melaye.

Amma jama'a na ci gaba da nuna turjiya.

Sai dai kuma Shugabannin kungiyar dalibai yan asalin jihar Kano a Najeriyar sun gudanar da wata kwarya kwaryar zanga zanga kan nuna adawarsu da cire tallafin man fetur din.

Daliban wadanda suka ce zanga zangar ta somin tabi ce, sun ce sun bada sa'o'i 24 ga gwamnatin kasar ta janye matakin ko kuma su gudar da wata gagarumar zanga zanga ta dukkan dalibai a fadin jihar gobe.

Yau da safe ma wasu matasa sun gudanar da wata makamanciyar wannan zanga zanga.

Yanzu haka dai tuni kudin sufuri a garuruwa da dama na kasar ya linka, sanadiyyar karuwar kudin mai a gidajen mai.

Wasu gidajen man dai na sayar da man ne a kan Naira 150 daga Naira 65 a kan kowacce Lita guda ta man.

A jiya ne dai Hukumar kula da kayyade farashin man fetur a Najeriya (PPPRA) ta sanar da cire tallafin man fetur daga ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2012.

Masu sharhi na ganin wannan na nufin daga yanzu, 'yan kasar za su rinka sayen man fetur a kan naira 143 ko makamancin haka kan kowacce lita guda.

Mai magana da yawun kamfanin mai na kasa NNPC Dr. Livi Ajuonoma ya tabbatar da daukar matakin ga BBC.

Wata sanarwa da hukumar ta PPPRA ta aikewa manema labarai, ta bayyana cewa an dauki matakin ne biyo bayan tattaunawar da gwamnati ta yi da masu ruwa da tsaki a lamarin.

"Muna fatan sanar da duk masu ruwa da tsaki a fannin man fetur cewa, daga yanzu an cire tallafin da ake bayarwa kan farashin man fetur, kamar yadda doka ta bamu ikon yi," a cewar PPPRA.

"Wannan sanarwa na nufin cewa gwamnatin ta janye hannunta daga harkokin tataccen man fetur.

Ana nuna damuwa

Kamfanonin man da ke sayar da mai na da ikon shigo da man sannan su sayar da shi kan farashin da ya dace da kasuwa - wanda za a rinka wallafawa duk bayan makwanni biyu".

Hukumar ta kuma ce masu ruwa da tsaki a harkar man fetur su sani cewa daga ranar 1 ga watan Janairun 2012, babu wani kamfani ko dan kasuwa da za a kara biya kudin tallafi kan man fetur din da ya shigo da shi.

A makonni masu zuwa hukumar ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da kuma tuntubar jama'a domin tabbatar da cewa komai na tafiya kamar yadda aka tsara ba tare da wata matsala ba.

Batun janye tallafin man dai na daga cikin abubuwan da suka dade suna haifar da cece-kuce a kasar, wanda kungiyoyin kwadago da na siyasa suka yi Allah wadai da shi.

Kungiyoyin na cewa janye tallafin zai kara jefa al'ummar kasar cikin matsanancin hali da kuma kuncin rayuwa.

Gwamnatin ta yi kiyasin cewa za ta samu karin kudaden da suka kai dala biliyan 8 daga janye tallafin, kuma ta ce za ta yi amfani da su ne wurin ayyukan ci gaban kasa.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen samar da danyan man fetur, amma tana shigo da man da take amfani da shi ne daga waje, sakamakon rashin ingantattun matatun mai da kuma tashe-tashen hankula.

Karin bayani