An gudanar da zanga-zanga a sassan Najeriya

Masu zanga-zanga a legas Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Daruruwan mutane sun hallara a babban dandalin taron jama'a na tsakiyar birnin Legas

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na Najeriya, don nuna adawarsu da janye tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.

Tun bayan bayar da sanarwar janye tallafin ranar Lahadi, farashin man fetur ya nunka fiye da sau biyu.

Wakilin BBC a Legas ya ruwaito cewa ya zuwa yanzu, daruruwan mutane sun hallara a babban dandalin taron jama'a na tsakiyar birnin, yayin da ake kona tayoyi a kan manyan tituna; ana kuma hana motoci wucewa.

Masu zanga-zangar sun kuma yi kokarin ganin kowa ya tsayar da duk wata harka.

Rahotanni sun ce 'yan sanda ba su dauki matakin tarwatsa masu zanga-zangar ba, hasali ma dai ba a ganinsu sai dai idan sun zo wucewa ko kuma wadanda ke gadin wadansu muhimman gine-gine.

Da yake jawabi ga masu zanga-zangar, Seun Kuti, dan shahararren mawakin nan Fela, ya yi Allah-wadai da janye tallafin, yana mai cewa:

“Ba za mu yarda da irin wannan ta’addanci na Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) ba. Ba yadda za a yi 'yan Najeriya su sayi man fetur a farashin iri da na Amurka alhali ba sa daukar mafi karancin albashi irin na mutanen Amurka”.

Sauran wuraren da aka gudanar da zanga-zangar sun hada da biranen Badun, Jihar Oyo; da Lakwajan Jihar Kogi; da Lafia, Jihar Nasarawa, da kuma Kano.

A birnin Ilori na Jihar Kwara kuwa, rahotanni sun tabbatar da cewa mutum guda ya rasa ransa yayin zanga-zangar; mai baiwa gwamnan jihar shawara a kan harkokin yada labarai ya shaidawa BBC cewa mutumin ya mutu ne yayin wani turmutsutsu.

Ranar Litinin 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zanga a babban birnin kasar, Abuja, da ma wasu wurare.

Sai dai kuma masu fafutuka sun ce an sako mutanen da 'yan sandan suka kama ranar Litinin din, ciki har da tsohon dan Majalisar Wakilai, Dino Melaye, wanda ke cikin jagororin zanga-zangar.

Shi kuwa wani mai fafutukar kare hakkin bila’adama a Legas, Mista Bobson Delije, ya fara yajin cin abinci ne, don ya nuna fushinsa ga matakin gwamnatin.

Gwamnatin kasar dai ta ce janye tallafin zai samar da kudaden da za a yi amfani da su don gudanar da shirye-shiryen magance talauci.

Ministan yada labarai na kasar, Labaran Maku, ya shaidawa BBC cewa za a kafa wani asusu wanda zai kula da kudaden ta hanyar da 'yan Najeriya za su samu damar sa ido a kan yadda ake kashe su.

"Shugaban kasa ya kafa wani asusu a karkashin jagorancin daya daga cikin fitattun 'yan Najeriya wadanda ake ganinsu da mutunci, Christopher Kolade, don su kula da kudaden su kuma rika yiwa 'yan Najeriya bayani a kan yadda ake kashe su", in ji Mista Maku.

Ya kuma kara da cewa: "Sauran mambobin kwamitin za su fito ne daga kungiyoyin al'umma da kungiyoyi masu zaman kansu, da kungiyoyin kwadago, da ma kafofin yada labarai".

Karin bayani