An samu mutane biyu da kisan wani bakar fata a Birtaniya

Hakkin mallakar hoto Getty

Wata kotu a London ta sami wasu mutane biyu da laifin kashe wani matashi bakar fata, , kusan shekaru 20 da suka wuce.

shara'ar dai ta yi tasiri matuka a kan zamantakewa tsakanin farar fata da sauran jinsuna a Birtaniya.

Kotun dai ta sami dukan mutanen biyu, David Norris da Gary Dobson, da laifin aikata kisa.

A shekara ta 1993 ne dai wani gungun matasa farar fata suka daba wa Stephen Lawrence wuka a lokacin da yake jiran wata motar safa a London.

Tun farko dai 'yan sanda sun gaza cafke wadanda ke da alhakin kisan, abun da har ya kai wani bincike ya gaano cewa 'yan sandan suna nuna wariyar launin fata.

Al'ammarin da ya sa aka kawo sauye-sauye a dokokin Birtaniya.