Kungiyoyin kwadago a Najeriya zasu cimma matsaya

Hakkin mallakar hoto facebook
Image caption Wasu masu zanga zanga akan janye tallafin man fetur a Najeriya

A yau ne gamayyar kungiyoyin kwadago a Najeriya za su gudanar da wani taro a Abuja inda za su fayyace dubarun da za su dauka domin kalubalantar janye tallafin mai da gwamnatin kasar ta yi.

A wata sanarwa da kungiyar kwadago ta NLC ta fitar jiya talata, kungiyar ta kuma jinjinawa 'yan Najeriyar wadanda suka gudanar da zanga a sassa dabam dabam na kasar.

Kungiyar ta kara da cewa ta daura alhakin tarzomar da aka samu wacce ta kai ga kisan wani mai zanga-zanga a birnin Illori akan gwamnatin tarayya, inda ta ce tun da farko ta riga ta gargadi gwamnatin da kada ta yi amfani da jami'an tsaro wajen hana zanga-zangar.

NLC ta ce mambobinta ba za su ja da baya ba, inda ta yi barazanar kai karar gwamnatin tarayya gaban kotun hukunta laifukan yaki ta duniya da ke birnin Hague akan duk wani cin zarafin jama'a.

To sai dai a martanin da ta mayar kan al'amuran da ke faruwa a kasar, Gwamnatin Najeriyar ta bukaci 'yan kasar da su dauki hakuri inda ta ce nan da wasu makwanni za su fara ji dadin matakin janye tallafin da gwamnatin ta dauka.