Beckham ba zai koma PSG ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon kyaftin din Ingila, David Beckham

Rahotanni daga Faransa na cewa tsohon kyaftin din Ingila David Beckham ya yanke shawarar kin komawa kungiyar Paris Saint-Germain saboda wasu dalilai da su ka danganci iyalinsa

Rahotani dai sun alakanta dan wasan da komawa kungiyar ta PSG bayan da kwantaraginsa da kungiyar Los Angeles Galaxy ya kare.

"Mun kasa cimma yarjejeniya, bamu ji dadin haka ba," In ji Direktan wasanni na PSG Leoardo.

"Saboda wasu dalilai da su ka danganci iyalin ne yasa dan wasan ya ki dawowa, kungiyar."

Tuni dai kungiyar ta PSG ta nada Carlo Ancelotti a matsayin kocinta.