Dubban 'yan kabilar Murle sun bar gidajensu

Sudan ta Kudu
Image caption Sudan ta Kudu

Rahotanni daga Sudan ta Kudu sun ce an kashe jamaa da dama a jihar Jonglei dake Gabashin kasar, sakamakon mummunan fadan da aka yi tsakanin kabilun Murle da Nuer, wadanda ba sa ga maciji da juna.

Wata maata 'yar kabilar Murle ta shaidawa BBC cewa an harbe danginta su 20 , bayan da suka gudu daga garin Pibor suka nemi mafaka a kusa da kogin Kengen.

A cikin 'yan kwanakin da suka wuce dai, dubun dubatar 'yan kabilar Murle ne suka tsere daga gidajensu a sakamakon hare-haren da mayakan Nuer suke kai musu.

Karin bayani