Yawan marasa aikin yi ya ragu a Amurka

Hakkin mallakar hoto Getty

Wasu alkaluma na ba zata da gwamnatin Amurka ta fitar sun nuna cewa a watan jiya, an samu raguwar marasa aikin yi da kashi takwas da rabi cikin dari, a karo na farko cikin kusan shekaru ukku.

Alkaluman sun nun cewa an samu karuwar sabbin ayyukan yi kusan dubu dari biyu a kasar.

Shugaba Obama ya yi marhabin da karuwar ayyukan yi a kasar, sai dai ya kara da cewa har yanzu akwai jan aiki dangane da rashin ayyukan yi a kasar.

Karin bayani