China ta maida Martani ga Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP

China ta gargadi Amurka kan kawo yaki a yankin pacific biyo bayan matakin da shugaba Obama ya dauka na ganin sun kara taka rawa a yankin.

Kamfanin yadda labaru na gwamnatin kasar Xinhau yace za'a yi marhaban da matakin Amurka idan manufarsu itace su inganta zaman lafiya ba wai su zo da wata akida na yaki ba.

Shugabannin Chinar basu fitar da wata sanarwa ba kan aniyar gwamnati Amurka akancewa zata kara karfin sojinta a yankin Asiya da pacific

Shugaba Obama dai ya bayyana wani shiri na yin kwaskwarima ga harkokin tsaron Amurka, lamarin da ya hada da rage girman rundunar sojin kasar.

Ya ce duk da kasancewar za a rage girman rundunar, amma Amurka zata ci gaba da kasancewa a kan gaba wajen karfin soji a duniya.

Masu aiko da rahotanni na cewa sabon shirin na Amurka ya yi la'akari da damuwar da ma'aikatar tsaron Amurka ke nunawa cewa ya zama tilas Amurkar ta yi la'akari da karfin fada-ajin da kasar Sin ke kara samu.

Sai dai hukumomin Amurka sun ce koda yake karfin sojin kasar zai ragu amma ya kamata duniya ta kwan da sanin cewa Amurka za ta kasance a kan gaba a duniya ta fuskar karfin soja.

Mr Obama ya ce Amurka za ta karfafa matsayinta a yankin Asiya da Pacific, kuma za ta cigaba da zuba jari a muhimman bangarorin da ta kulla kawance a kansu, ciki har da kungiyar tsaro ta NATO.

Karin bayani