Kungiyoyin kwadago sun kira yajin aiki

Karin farashin mai zai janyo yajin aikin gama gari a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Karin farashin mai yai janyo hauhawar farashin kayyaki da na sufuri a Najeriya

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a Najeriya sun yanke shawarar fara yajin aikin gama-gari a ranar litinin mai zuwa don nuna rashin amincewa da cire tallafin mai da gwamnatin kasar tayi.

Kungiyoyin kwadagon za su tafi yajin aikin sai baba ta gani. Shugabannin kungiyoyin kwadagon sun yanke hukuncin tafiya yajin aikin ne bayan wata ganawa da sukayi yau.

Gwamnatin Najeriyar dai ta janye tallafin mai a ranar lahadin da ta gabata abinda ya sa farashin mai akan lita ya tashi daga naira 65 zuwa naira 144.

Miliyoyin 'yan Najeriya ne dai ke fama da matsanancin talauci, inda suke rayuwa a kasa da dalar Amurka daya a rana.