Kotu a London ta daure faren fata kan kisan baki

Stephen Lawrence Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stephen Lawrence

Wata kotu a London ta yankewa wasu mutane biyu fararen fata hukuncin dauri, bayan samunsu da laifin kisan wani matashi bakar fata, kusan shekaru 20 da suka wuce.

Kotun ta yankewa Gary Dobson hukuncin daurin akalla shekaru 15 da watanni 2, yayinda David Norris kuma aka yanke ma sa hukuncin dauri na akalla shekaru 14.

Sai dai mahaifiyar Stephen lawrence wanda aka kashe, Doreen ta ce duk da cewa hukuncin ba mai tsauri ba ne amma ta yi fahimci cewa kotun ta fuskanci sarkakiya ganin cewa wadanda aka samu da laifin sun aikata hakan ne lokacin suna da karancin shekaru.